DALILIN WANNAN TARAYYA
AL-AQARIB FOUNDATION AZARE an assasa shine don ya saukaka wa kowane dan uwa daga cikin dangi taimakawa Dan uwansa, ta hanyar bada sadaka da zamu ajiye a asusu, don idan muhimmiyar bukata ta taso ataimaka. Duk wanda kaganshi a ciki, akwai babbar alaka da ta hadaka/ki dashi ta dangin nesa ko kusa. Allah yabar zumunci ya kara daukaka. Amin
DOKOKIN AL-AQARIB FOUNDATION
- Tallafi za’ake bayarwa ba magance matsala gaba daya ba
- babu bada aron komai
- bawanda za’a bashi/ta tallafin daya wuce sau 3 a shekara, sai dai a rashin lafiya mai tsanani.
- jagorori bazasu nemi tallafi ba sai dai a rashin lafiya mai tsanani.
- tallafi za’a bawa wanda yayi regista ne kawai.
- idan lokacin hidimar azumi ko Sallah tazo, za’a duba masu karamin karfi a family abasu taimako
- Duk yara marayu a family, da suke da regista za’a sasu a tsari na musamman na taimakon marayu.
- Tallafi mafi karanci N5,000 ne. Za’a bada kudi ko kayan kudi.
- Asusun tallafi ako da yaushe bazaiyi kasa da Rabin abunda yake Asusun ba, bayan an bada tallafin watan.
- watan Azumi idan yazo kowane mai regista mai iyali, zai iya samun abun azumi idan asusun zai dauki nawin haka.
- jogorori zasu rike ragamar ne na tsawon she kara biyu. Ba zaben shuwagabanni, sai dai duba cancanta a cikin ko wane zuri’a za’a dauki mutum daya sai mutum uku a cikin wanda suka assasa.
- za’a samu komitin binciken yadda ake bada tallafi, wanda sai sun bada bayani ko wane wata kamin a bada tallafi
- sai anyi bincike kamin komitin bada tallafi su zauna zartarda hukunci akan bukatun da aka tura musu. Duk wanda bai samu ba sai ya kara nema a wani wata.